Bankin Duniya ya bayar da tallafin N31.6m domin bunkasa karatun ‘ya’ya mata a Zango

Babban bankin duniya ya bayar da tallafin naira miliyan talatin da daya da dubu dari shida N31.6m domin kara bunkasa karatun  ‘ya’ya mata a karamar hukumar Zango dake nan cikin jihar Katsina . Kamfanin dillancin labarai ‘NAN’  ya rawaito cewa za a yi amfani da miliyan N14.8, wajen gyara da bunkasa  makarantun dake cikin karamar hukumar, haka kuma miliyan N16.8m za a yi amfani da su wajen bayar da tallafin karatu. An samar da kudaden ne karkashin bankin duniya a sashen UNICEF ta fannin shirin daidaita tasu wajen ilimi a duk…


Read More

Kwamishiniyar lamuran matan jihar Katsina ta yi ruwan makudan kudade, ga wasu yara da mata

Kwamishiniyar lamuran mata ta jihar Katsina Dr. Badiya Hassan Mashi ta raba makudan kudade ga wasu kananan yara da kuma mata masu lalura a tare da su Daga cikin wadanda suka amfana da tallafin akwai Umaima mai shekaru 10 da haihuwa, wadda Allah Ya jarabta da lalurar ciyon koda, da ta sami taimakon naira dubu hamsin 50,000, tare da bayar da tallafin naira 50,000 Khadija Umar da ta sami lalurar C’S a lokacin haihuwa Haka kuma Kwamishinar Basariya Ibrahim yar shekaru 5 wadda ke a kauyen Birnin Kuka wadda ita…


Read More

Masari zai gina hanyoyi a kan kudi naira biliyan N23.6b

Gwamnan jihar Katsina Rht Hon Aminu Bello Masari ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ware naira biliyan N23.6b domin shinfida hanyoyi na tsawon kilo mita 226.3km a duk fadin jihar Katsina. Gwamnan ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter, inda ya nuna cewa za a gina tare da gyaran  hanyoyin ne domin samar da ingattattu kuma nagartattun hanyoyi a duk lungu da sakon jihar Katsina. Gwamnan ya kuma bayyana cewa gyaran hanyoyin zai rage radadin talauci ga mutanen kankara, tare da matso da su cikin tafiya daidai da zamani….


Read More

Malaman Firamare sun sami karin girma a Jihar Katsina

  Gwamnatin jahar Katsina ta yi karin girma na shekara uku ga malaman makarantun firamare da ke fadin jahar. Gwamnan jahar katsina Aminu Bello Masari ne ya sanar da hakan a wajen wani bikin yaye dalibai da bayar da kyaututtuka wanda ya gudana a firamaren Ida da ke birnin katsina jahar katsina arewa maso yammacin Najeriya. Gwamna Masari wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar Ilmin bai daya (SUBEB) ta jahar, Malam Lawal Duhari Daura ya bayyana cewa Karin girman ga malaman wani bangare ne na basu kwarin gwiwa domin su…


Read More

Dole a sanya katin tantance masu kada kuru’u a zaben dake tafe na kananan hukumomin jihar Katsina – Majalissa

Majalisar jihar Katsina ta gabatar da kudurin yin zaben kananan hukumomi sa katin tantance masu kada kuru’u wanda a turance ake kira ‘Card Reader’ Shugaban kwamitin sashin tsarin mulki na majalissar Hon. Murtala Ado Kaita shi ne ya karanta kudurin a zauren majalissar, wanda ya sami amincewar sauran yan majalisun. Shi ma a nashi jawabin shugaban masu rinjaye na majalissar Hon. Hambali Faruk Katsina ya ce kudurin na kan hanyar da za ta kara martaba darajar zabe a jihar. Daga karshe kakakin majalissar Rht Hon. Abubakar Yahya Kusada ya ce…


Read More

CANJIN RAYUWA [Kashi na Uku] Tare da Halima K. Mashi (Shafi na 51 – 60)

Ismail yace, ba zaki yi magana a saki ba mimi? Yaya Amina tace, haba Ismail, Kalli yadda take mana qafafu a sagale taya za’a sata tayi fitsari? Yace hakane. To ynxun sai dai ta dinga yi a kwance? Yaya Amina tace, dole a samu robar fitsari, amma mu nemi Shawarar likitan. Ismail yace, to zan sameshi. Amma ynxun ya kk ganin za’ayi gurin cire mata kayan? Ko inje in fara dauko mata wasu in dawo? Yaya Amina tace, to kayi sauri don inason inje gida sbd abincin dare. Insha Allahu…


Read More

Su waye ‘Yan dumama kujera a majalissar tarayya , cikin ‘yan majalissu 15 dake wakiltar Katsina a majalissar tarayya?

Jihar Katsina jiha ce da take da yawan Wakilai a majalissar wakilai ta tarayya Abuja, da suka kai kimamin guda goma sha biyar (15) dake wakiltar kananan hukumomin da muke da su a duk fadin jihar Katsina. Sai dai kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa a ranar  10-8-2017 ta buga, binciken jaridar ya gano cewa  ‘Yan majalisar tarayya goma sha biyu (12) cikin sha biyar  (15)  na  jihar Katsina ba su taba gabatar da kuduri (Bill)  ko guda daya ba a zauren Majalisar,  cikin shekaru biyu da suka yi…


Read More

Gwamna Masari zai kafa gidajen radiyo na FM guda uku a jihar Katsina

Gwamnan jihar Katsina Rht Hon Aminu Bello Masari zai kafa gidajen rediyo na FM har guda uku a cikin jihar Katsina. Shugaban gidan rediyon jihar Katsina Alhaji Sani Bala, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya je ziyarar mika ta’aziya a fadar Masarautar Daura bisa rasuwar Alhaji Hamisu Haruna wanda babba ne a majalissar Sarkin. Alhaji Sani Bala ya ce za a kafa sabbin gidajen rediyon ne a shiyar Katsina da Daura da kuma shiyar Funtua. Ya bayyana cewa kafa sabbin gidajen rediyon zin taimaka wajen wajen samar da ayyukan…


Read More

Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa kwamitin da zai jagoranci bikin murnar cika Katsina shekara 30 da kirkira

Gwamnatin Jihar Katsina ta rantsar kwamiti mai mambobi 26 karkashin jagorancin sakataren gwamnatin jihar Katsina Dr Mustapha Inuwa, domin jagorantar bikin murnar cika shekara 30 da kafa jihar Katsina. A lokacin kaddamar da kwamitin, shugaban kwamitin Mustapha Inuwa ya yi kira da sauran membobin kwamitin da su bayar da dukkanin hadin kai wajen tabbatar an gudanar da bikin cikin nasara. Kwamitin ya kunshi wakilan jami’an tsaron dake cikin jihar da, kwamishinan Yada Labarai, da na Kasuwanci, da na Ayyuka, da na Wasanni da kuma Kwamishinar lamuran Mata da kuma Sarkin…


Read More